Ministan Sufurin jiragen sama ya bayyana cewa za afara zirga-zirgar jiragen sama na kasa-da-kasa daga ranar 29 ga Agusta.
Sirika ya ce filin jirage saman Abuja da Legas ne za su fara aiki tukunna.
Wannan sanarwa na kunshe ne a jawabin da miniista Sirika yayi a taron kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar Korona a Najeriya, ranar Litini.