Rashin biyan hakkunan mamata da ‘giratuti’: Muna cikin tsananin talauci a Kano – Kira ga Gwamnatin Kano

0

Mutane da dama da suka zanta da PREMIUM TIMES Hausa a Jihar Kano sun koka matuka bisa yadda gwamnatin jihar Karkashin Gwamna Umar Ganduje ya yi watsi da biyan su hakkunan iyayen su da suka rasu suna wa gwamnatin jihar aiki da wadanda suka yi murabus a aiki.

Da yake zantawa da wakilin mu a Kano, wani wadda ma haifin sa ya rasu yana aikin gwamnati a jihar ya shaida mana cewa lallai shi da ‘yan uwansa na cikin wani hali na kunci a rashin biyan su iyalan mamacin hakkin mahaifin sa da ya rasu.

” Ina so in ankarar da Gwamnati tare da sanar da ita irin mawuyacin halin da iyalan maikatan da suka rasu suna aiki suke ciki a sakamakon kin biyansu hakkokinsu na wanda ya rasu wato ‘ Death Benefits’ da Gwamnati batayi akan lokaci.

” Ya kamata Mai girma gwamna da Yan majalisunmu na jihar Kano su sani, rayuwa da tarbiyya ta wadannan iyali tana tabarbarewa tare da abkawa mawuyacin hali wadda takan kaiwa har mutuwa a dalilin yunwa, rashin mahalli a sakamakon ba kudin da za’a biya kudin haya, rashin suttura dadai sauran abubuwan da suka zama dole na tafiyar da al’amuran rayuwa.

” Gwamnati ta sani iyalan ma’aikatan da suka rasu tun daga 2016 har kawo yau basu samu hakinsu na ‘Ma’aikacin da yasu yana aiki ba wato ‘Death benefits’ da doka tace a basu ba, wanda a dalin haka da yawansu sun dole suka hakura da zuwa makaranta, wasu suka koma mabarata, ‘Yan maula, ‘yan shaye-shaye dadai sauransu.

Bincike ya nuna cewa ba tun darewar wannan gwamnati bane aka fara samun matsalar rashin biyan wadannan kudade ga iyalan mamaci, da wadanda suka bar aiki a jihar Kano, amma abin tambaya shin wannan Gwamnati wanne kokari take domin magance wannan matsalar?

Masu jiran giratuti sun koka cewa a lokutta da dama sun ji an kafa kwamitoci har wajen kala biyar domin shawo wannan matsala, amma har yanzu basu ji gwamnati tayi wani abin azo a gani ba iyalai kuma na ta wahala.

Wasu da suka tofa albarkacin bakin su game da wannan matsala ta rashin biyan ‘yan Fansho a jihar Kano sun shawarci gwamnati da maimakon jibga kudade da take yi wajen gine-gine, gina al’umma yafi tukunna, da nan sai a raya kasa.

” Wallahi rayuwar mutanen dake salwanta a dalilin matsalar rashin biyan hakkunan su yafi matsalar da rashin gada ko wawukeken titi ke haifarwa illa.

A karshe sun bada shawarar cewa ” Idan har Gwamnati bata da wadatattun kudin da zata warware matsalar lokaci guda to ta ta fara biyan iyalen maaikatan da suka rasu kafin wadanda suka bar aiki domin su wadanda suka ajiye aiki Gwamnati na kokari tana biyansu pension duk wata.

Wani jami’a a gwamnati Kano da baya so a fadi sunan sa saboda ba a bashi damar yin haka ba ya bayya na cewa lallai gwamnatin Gwmna Abdullahi Ganduje na kokarin ganin duk an warware wannan matsala. Ya ce gwamnatin ta kafa kwamitoci a baya domin kawo karshen matsalaririn haka kuma lallai za a ga hubbasan gwamnati. Domin masu karbar Fansho sun a samun albashin su.

Share.

game da Author