Korona dai ta dauko hanyar yin Sallama da Najeriya, an samu karin mutum 288 kacal ranar Litini

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 288 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litini.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –88, Kwara-33, Osun-27, FCT-25, Enugu-25, Abia-20, Kaduna-17.

Filato-13, Rivers-13 Delta-10, Gombe-8, Ogun-4, Oyo-3, Katsina-1 da Bauchi-1.

Yanzu mutum 44,129 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 20,663 sun warke, 896 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,570 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,355 FCT – 3,997, Oyo – 2,771, Edo – 2,311, Delta – 1,520, Rivers 1,842, Kano –1,597 , Ogun – 1,407, Kaduna – 1,498, Katsina –745, Ondo – 1,204 , Borno –613, Gombe – 612, Bauchi – 561, Ebonyi – 808, Filato – 1,240, Enugu – 846, Abia – 582, Imo – 469, Jigawa – 322, Kwara – 786, Bayelsa – 339, Nasarawa – 339, Osun – 580, Sokoto – 153, Niger – 224, Akwa Ibom – 221, Benue – 356, Adamawa – 164, Anambra – 135, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 152, Taraba- 54, Kogi – 5, da Cross Rivers – 58.

KIRA GA MATASA: Cutar Korona har kisa ta na yi idan ta Kama matashi – Shugaban WHO

Shugaban Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya Tedros Ghebreyesus ya gargadi matasa da ke cewa kwayoyin cutar Korona ba zai iya kama su ba da su daina wannan zato, yana mai cewa ba kama matashi ba ma kawai har kisan sa zai iya yi idan bai kiyaye ba.

Bayan haka kuma ya shaida cewa lokaci yayi da kasashen duniya za su koyi shirin zama dindindin da kwayoyin cutar Korona.

Dole ne mu koyi rayuwa da wannan cuta tare da ɗaukar matakai domin mu rayu, tare da kare kanmu da sauran jama’a.

Sannan kuma ya yabawa kasar Saudiyya kan irin matakan da ta ɗauka yayin gudanar da Aikin Hajjin bana.

Share.

game da Author