Jihohin Kaduna, Kwara da Abuja sun bayyana ranakun bude makarantu domin daliban ajin karshe su rubuta jarabawar karshe.
Idan ba a manta ba an rufe makarantun kasarnan tun a watan Maris saboda barkewar annobar Korona.
Bayan sasantawa da hukumar jarabawa ta WAEC gwamnatin tarayya gwamnati ta amince a bude wadannan makarantu domin dalibai su rubuta jarabawar su na kammala sakandare.
Jihar Kaduna
Kwamishinan ilimi ta jihar Kaduna Shehu Makarfi ya bayyana cewa gwamnati ta tsaida ranar 10 ga watan Agusta ranar da daliban ajin karshen Sakandare wato SS3 za su dawo makarantun su a jihar.
Ya ce gwamnati ta bada tazaran mako daya kafin a fara rubuta jarabawar domin makarantu su saka matakan kiyaye kamuwa da Korona.
“Makarantun sakandare na kwana za su fara aiki ranar 9 domin karban daliban da za su dawo.
Makarfi ya ce gwamnati za ta sanar da ranar da sauran dalibai za su dawo makarantu a jihar, amma kafin haka dalibai za su ci gaba daukar darasi ta yanar gizo.
Jihar Kwara
A jihar Kwara kuma Dalibai za su dawo makaranta ranar 5 ga watan Agusta.
Kwamishinan ilimi na jihar Hajia Bisola Ahmed ta bayyana cewa gwamnati ta bada takunkumin fuska guda 65,000 domin a raba wa wadannan dalibai dake shirin rubuta jarabawar kammala makarantar sakandare.
Bisola ta ce ma’aikatar ilimi za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki a fannin domin raba wa makarantun man tsaftace hannu. Sannan gwamnati ta dauki matakan da za su taimaka wajen ganin duk makarantun sun kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar covid-19.
Abuja
Hukumar babban birnin tarayya ta bayyana cewa daliban dake ajujuwan SS3 da JSS3 za su dawo makaranta ranar 4 ga watan Agusta.
Dokokin Korona da jihohin suka gindaya.
Duka jihohin dai sun saka dokoki da makarantu za su kiyaye domin gujewa kamuwa da Korona akamar haka:
1. Sai anyi wa duka makarantun feshi kafin a bude su.
2. Duk da cewa gwamnati za ta raba takunkumin fuska da man tsaftace hannu wa dalibai suma iyaye su tabbata sun wadata ‘ya’yan su da takunkumin fuska da man tsaftace hannaye.
3. Makarantu za su tanadi na’urar gwada yanayin jikin dalibi a lokacin da ya shigo makaranta.
4. Makarantu za su tsara yadda za ayi jarabawa ba tare da an gwamatsu a wuri daya ba.
5. Dole iyaye su tsara yada za su kawo da daukan ‘ya’yan su daga makaranta.
6. A karshe kuma mahukuntar makarantun za su rika sa ido domin ganin an gaggauta sanar da NCDC idan aka lura wani ya nuna alamun rashinlafiya.