KORONA: Mutum 325 suka kamu ranar Asabar, mutum daya ya rasu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 325 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –87, FCT-49, Gombe-28, Ebonyi-20, Filato-19, Kwara-18, Enugu-17, Imo-12, Rivers-12, Kaduna-11, Ogun-10, Edo-9, Oyo-9, Ondo-8, Osun-8, Ekiti-4, Borno-1, Kano-1, Bauchi-1 da Nasarawa-1

Yanzu mutum 48,770 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 36,290 sun warke, 974 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,506 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 16,456 FCT – 4,714, Oyo – 2,952, Edo – 2,423, Delta 1,639, Rivers 2,005, Kano –1,678, Ogun – 1,545, Kaduna – 1,755, Katsina –746, Ondo 1,381 , Borno –703, Gombe – 676, Bauchi – 582, Ebonyi – 931, Filato 1,708, Enugu – 997, Abia – 677, Imo – 506, Jigawa – 322, Kwara – 906, Bayelsa – 352, Nasarawa – 374, Osun – 737, Sokoto – 154, Niger – 229, Akwa Ibom – 246, Benue – 430, Adamawa – 185, Anambra – 156, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 204, Taraba- 78, Kogi – 5, da Cross Rivers – 73.

Mutum sama da milyan daya sun kamu da korona Nahiyar Afrika

Ofishin WHO dake Brazzaville kasar Kongo ta bayyana cewa mutum sama da miliyan daya sun kamu da cutar Korona a Afrika.

Yankin Afrika na daya daga cikin nahiyoyin da a duniyan korona ta yi wa mummunar kamu.

A yanzu dai kusan mutum miliyan 20 a kasashe sama 200 a duniya sun kamu da cutar.

An yi hasashen cewa lallai wannan cuta za ta yi wa yankin Afrika din mummunar Kamu saboda rashin ingantattun kiwon lafiya da kuma tsananin talauci da ake fama dashi a yankin.

Koma Bayan tattalin Arziki

Cutar Korona ta yadu zuwa kasashe 54 dake Nahiyar kuma mutane da dama sun rasa rayukan su sannan kasuwanci da na kai komo duk sun ruguje.

Binciken da tarayyar kasashen Afrika ta yi AU ya nuna cewa mutum miliyan 20 za su iya rasa aikin su a Afrika.

Sannan manya-manyan kasashen dake da arzikin man fetur kamar Najeriya da Angola za su yi asarar dala biliyan 65.

Domin guje wa irin haka ne gwamnatocin kasashen Afrika suka fara sassauta dokar hana walwala da aka saka domin dakile yaduwar a kasashen domin rage radadin talauci na Korona.

Sannan kuma akwai yiwuwar wasu da dama za su rasu, wasu kuma su kamu da ita kanta Korona din amma kuma basu sani ba.

Share.

game da Author