Hukumar yaki da safarar mutane ta kasa ta damke wani lebura mai suna Lawali Bala dake zaune a kauyen Rikina karama Dange/Shuni, jihar Sokoto da ake zargin ya bata wasu yara kanana har 12 ta hanyar yin lalata da su ta baya.
An gano cewa Lawali na yin fasikanci da yara maza har har su 12 idan iyayen su sun yi barci da dare.
Darektan NAPTIP na shiyyar Sokoto, Zamfara da Kebbi, Mitika Mafa-Ali, ya bayyana haka da yake hira da wakilan kamfanin dillancin labaran Najeriya, a garin Sokoto.
Ali yace wannan Lebura yana yi wa iyayen wadannan yara aiki ne. ” A haka ne ya rika yin fasikanci da yaran maza sannan yana koya musu dabi’ar yin luwadi a lokacin da iyayen su ke barci.
An dai tabbatar da cewa wannan gabadayan su yaran su 12 yakan bi su inda suke kwance ya tattago su zuwa inda yake ya yi fasikanci da su.
Daya daga cikin mahaifiyar ‘yayan ta sahida cewa an taba kai shi kara ofishin Hisbah kafin akai ga sanar da hukumar NAPTIP abinda yake yi, har suka kama shi.