Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ba jami’ar NOUN ta Najeriya da ake karatu ta yanar gizo ta gina wurin daukar darasi a jihar.
Bayan haka kuma gwamna Matawalle ya ce zai zai dauki nauyin yara 200 domin karatu a wannan jami’a.
” Wannan hanya ce da zai kara fadada harkar ilimi ga yaran jihar Zamfara. Tun da na zama gwamnan wannan jihar na dauki nauyin mutum 200 domin su yi karatu a darussan kiwon lafiya da fasaha a jami’o’in kasashen waje saboda karfafa fannin kiwon lafiya da fasaha a jihar.
Daga nan Matawalle ya ce burin inganta fannin ilimin jihar na daga cikin dalilan da ya sa gwamnati ta ware kaso mai tsoka a kasafin kudin bana domin tabbatar da hjakan a auku.
Shugaban jami’ar NOUN Farfesa Abdallah Adamu ya ce jami’ar na daukar dalibai, koyar dasu sannan da shirya jarabawa duk a yanar gizo, wato Intanet.
“A Yanzu haka dalibai ‘yan yankin Arewa 17,000 ne kacal ke karatu a jami’ar. hakazalika ko a wajen neman karin daukan malamai da jami’ar ta yi, cikin mutum 400 da suka nemi aikin malunta a jami’ar, mutum 9 ne kacal daga yankin Arewa.
Farfesa Abdallah yayi kira ga gwamnonin Arewa da su maida hankali matuka wajen bunkasa ilimi a jihohin su domin ci gaban Arewa da kasa baki daya.
Discussion about this post