Boko Haram na daukar kananan yara sabbin sojojin sunkurun kungiyar – Rundunar Hadin Guiwa (MNJTF)

0

Rundunar Sojojin Taron Dangin Yaki da Boko Haram ta Kasa-da-kasa (MNJTF) ta bayyana cewa yanzu kuma Boko Haram sun fi maida hankali ne wajen tirsasa wa kananan yaran da suke kamawa shiga aikin soja, domin kungiyar ta dawo da karfin ta wanda sojoji suka karya mata alkadari a Yankin Tafkin Chadi.

Kakakin Yada Labarai na MNJTF, Timothy Antigha ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar da ya fitar s N’Djamena, babban birnin kasar Chadi a ranar Alhamis.

Kanar Antigha da ke sojan Najeriya, ya ce Boko Haram sun karkata wajen tirsasa wa yara kanana shiga sojan sunkurun ta’addanci, ganin yadda mambobin kungiyar ‘yan ta’adda sai mika wuya suke yi ga sojoji su na saranda.

Ya ce wannan labarai mai ban takaici ya zo musu ne a matsayin wani labarin sirri da sojoji suka samu a wata kwakkwarar majiya kuma wasu kungiyoyi sun kara tabbatar da haka.

Antigha ya kara da cewa su kan su Boko Haram din sun tabbatar da cewa su na daukar kananan yaran, domin akwai dimbin kananan yara a cikin bidiyon da Boko Haram suka watsa a ranar Sallah.

A cewar sa, “Boko Haram sun bijiro da sabuwar hanyar azabtar da kananan yara wajen rashin tausayin su da suke yi, ana ba su makamai su yi yaki domin a tayar da tarzomar bijire wa gwamnati.”

“A baya can Boko Haram sun fi bada karfi wajen kamen daliban sakantare mata, tirsasa su yin lalata da su da kuma kisan-gilla kan jama’a.

Ya shawarci matasa su rika yijn kaffa-kaffa daga fadawa hannun masu mummunar ta’addanci.

Share.

game da Author