Gwamnatin Tarayya za ta zabtare kudaden jihohin da suka rubanya wa kamfanonin sarrafa ma’adinai haraji

0

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta zabtare kudaden da ta ke bai wa jihohin da suka rika karbar harajin kamfanin sarrafa ma’adinai kuma suka bar kananan hukumomi su ma na karbar haraji dag kamfanonin.

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka, bayan Ministan Harkokin Ma’adinai da Karafa, Lekan Adegbite ya gabatar da wani ba’asin neman amincewa ga Majalisar Zartaswa inda ya nemi amincewar a ba shi izmi domin ya gudanar da gyare-gyare a kalubalen da Ma’aikatar Harkokin Ma’adinai ta Kasa.

Adegbite ya lissafa kalubalen da harkar ma’adinai ke fuskanta, ciki har da yadda jihohi da kananan hukumomi ke karbar karbar haraji daga kamfanonin harkokin ma’adinai.

Adegbite ya ce wannan matsalar ita kadai ke sa masu son zuba jari ke kyama da kuma kaurace wa zuba jari a Najeriya.

Da ya ke magana da manema labarai bayan tashi daga taron zartaswa, Lai ya kara nuna cewa, “Majalisar Zartaswa ta umarci Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed cewa daga wannan wata duk jihar da ta rika karbar haraji daga kamfanonin sarrafa ma’adinai, to za a rika cirar kudaden daga hannun jihohi.

Ya ce darasin koyo a nan shi ne Gwamnatin Tarayya ba ta so masu zuba jari su na kaura daga cikin Najeriya.

Sannan kuma ya ce akwai gagarimar matsalar rashin tsaro a wasu yankunan da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Share.

game da Author