Gwamnatin Tarayya ta roki manyan kasashen duniya su yi watsi da bayanan soki-burutsu ko tsayawa tankiya da gardandami su na hana Najeriya makaman da za su yi yaki da Boko Haram.
Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a wata tattaunawar musamman da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) suka yi da shi, ranar Alhamis a Abuja.
“Ina so na yi amfani da wannan dama na bayyana cewa manyan kasashen duniya da su iya kara kaimin taimakon da suke yi mana, fiye da wanda suke yi a yanzu.
“Shi yaki sai da makami. Don haka idan har muna son yin galaba kan Boko Haram, to fa sai da manyan makamai.
“Matsawar manyan kasashen duniya za su bi rudun masu tayar watsa labaran batunci kan Najeriya su kaffa hujja da su, su rika hana mu makamai, to a daina korafin cewa Najeriya ta kasa wajen dakile Boko Haram.
Lai ya ce akwai wasu kasashe a duniya da hatta makamai wadanda za mu yi yaki da su, duk daina sayar mana suka yi.”
Yayin da ministan bai ambaci sunayaen kasashen ba, ya kara da cewa, “mun biya kudin makamai da kayan gyaran makamai, an ki kawo mana kayan yaki ki ba mu kudin mu. Sannan kuma ko kayan gyara ma ba su rama mana ba.
“Ni kiran da zan yi wa wadannan kasashe shi ne su dubi kalubalen da ke gaban Najeriya, ta basu makamai domin mu samu mu ragargaji ‘yan ta’addanci..
Lai ya yi korafin cewa ‘yan Najeriya ba su gani, kuma ba su jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari kan kokarin sa na shawo kan kashe-kashen ta’addanci.
Ya ce ya kamata a rika auna irin tabarbarewar tsaro tun daga 2015, to za a iya fahimta kan irin ci gaba da gwamnatin Buhari ta samu a yanzu.
Discussion about this post