BINCIKEN MAGU: Sagay ya tofa wa Kwamitin Salami yawun barci, ya ce bai gamsu da mutanen da aka nada a kwamitin ba

0

Shugaban Kwamitin Mashawartan Shugaban Kasa Kan Rashawa, Farfesa Itsay Sagay, ya yi tofin rashin gamsuwa da yanayin mutanen da aka saka matsayin Mambobin Kwamitin Ayo Salami masu binciken zargin cin hanci da rashawa da karkatar da kudaden da ake yi wa tsohon shugaban rikon Hukumar EFCC, Ibrahim Magu.

Sagay ya ce bai taba ganin irin kakudubar bincike ba, inda za a rika kiran masu zargin Magu a bayan idon sa, sannan kuma a hana shi kwafen takardun bayanan binciken da ake yi masa, ballantana ya yi shirin kare kan sa kafin ya je gaban kwamitin bincike.

Rahotanni sun tabbatar Sagay ya ce, “a bisa dukkan alamu, dukkan ‘yan kwamitin kakaf din su Mai Shari’a Ayo Salami ne kadai adali a cikin su, wanda kuma ba wata boyayyar manufa ya je karewa ba.”

“Ina kalubakantar Kwamitin Ayo Salami, saboda yadda ya ke gayyatar masu zargin Magu ana karbar hujjojin da su ke bayarwa, ko kuma na ce zargi. Amma Kuma ba za a bai wa Magu kwafen zarge-zargen da ake yi masa ya gani ba, ballantana ya yi shirin kare kan sa.

“Sannan kuma baya ga rahotannin da mu ke karantawa, kwamitin cike ya ke fal daga DSS, Ma’aikatar Shari’a da sauran hukumomin tsaro. Alhali kuma su dai ne masu zargin sa din dai.

“Mai Shari’a Salami ne kadai wanda ba ya tare kowane bangaren masu zargin Magu.

“Kotun Koli ta taba tsine wa irin wannan kwamiti da aka taba kafawa a kan Gani Fawehinmi a cikin 1985. Domin ‘yan kwamitin su ne masu zargin sa.

“Amma na yi imani cewa Mai Girma Tsohon Mai Shari’a Ayo Salami ya na da nagarta da kima da darajar da ba zai taba yarda wasu ‘yan bankaura su yi amfani da rashin gaskiya su zubar masa da mutunci ba. Duk kuwa da irin rubabi-rubabin ‘yan kwamitin da ke cikin aikin binciken.”

Wata wasika ta bayyana wadda ke dauke da sunayen mutum bakwai da ke cikin kwamitin na Salami, masu binciken Magu.

Akwai Ayo Salami, tsohon shugaban Kotun Daukaka Kara ta Kasa (Arewa ta Tsakiya); Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Micheal Ogbezi (Kudu maso Kudu); wakilin Ma’ikatar Harkokin Shari’a, Muhammad Babadoko (Arewa ta Tsakiya); wakilin DSS, Hassan Abdulalhi (Arewa ta Tsakiya).

Sauran su ne Muhammdu Shamsuddeen daga Ofishin Akanta Janar ta Tarayya (Arewa maso Yamma); Douglas Egweme, daga Ofishin Sa-ido Kan Sirrikan Hada-,hadar Kudade (Kudu maso Gabas) da kuma Kazeem Atitebits, wanda shi ne Sakataren Kwamiti (Kudu maso Yamma).

Share.

game da Author