Kungiyar kwallon raga ta Najeriya (BFN) ta nada fitaccen dan jarumin fina-finan Hausa na Kannywood Ali Nuhu jakadan kwallon Raga ta Najeriya.
Kungiyar ta ce ta yi haka ne a shirin nada jarumai kamar Ali Nuhu da sauran jaruman Najeriya ire-iren jakadu kamar haka domin bunkasa wasar raga a kasar nan.
Kungiyar BFN ta ce ganin yadda Ali Nuhu ya zama fitaccen jarumin fina-finan Najeriya musamman a yankin Arewa ya sa ta nada shi domin mutane daga musamman yankin Arewa su rika buga wannan wasa.
Bayan haka kungiyar ta nada wasu fitattun ‘yan Nollywood Jakadon kwallon raga domin wayar da Kan mutane game da kwallon ragan.
Wadannan fitattun sun hada da Ali baba, Mozez Praiz, Kunle Bamtefa, DJ Jimmy Jatt, Sound Sultan da Kunle Afolayan.
Babban burin kungiyar shine ci gaba da nishadantar da mutane ta hanyar hada wasanni da nishadi a kasar nan.
Hakan zai taimaka wajen sa mutane su san akwai was irin haka, wato wasan kwallon raga.
Shugaban kungiyar Francis Orbih ya ce yana sa ran cewa nada Ali Nuhu da kungiyar ta Yi zai taimaka wajen karkato da hankulan sauran fitattun ‘yan fina-finai zama jakadu domin wayar da kan mutane su san wasan kwallon raga a Najeriya.
Discussion about this post