Ma’aikatar jinkai ta bayyana cewa mutum miliyan biyar ne suka neman aikin N-Power a kasar nan.
Ministan ma’aikatar Sadiya Farouq ta sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Talata.
Sadiya ta ce an bude shafin cika fom din N-Power a yanar gizo ranar 26 ga watan Yuni Kuma aka rufe ranar 26 ga watan Yuli sannan daga baya aka kara makonni biyu domin wadanda basu samu cika fom din ba a baya su cika.
“A lissafe dai matasa 5,042,001 ne suka nemi aikin N-Power guraben mutum 400,000.
Minista Sadiyya tace wadanda suka cancanta za a ba gurbin aikin N-Power din.
“Hukumar za ta bada karfi wajen ganin Mata da nakasassu suka fi samun aikin.
Idan ba a manta ba a ranar 26 ga watan Yuli darektan yada labarai na ma’aikatan jinkai, Rhoda Iliya, ta bayyana cewa akalla mutum sama da milyan 5 ne suka cika fom din neman aikin N-Power a Najeriya zuwa yanzu.
Tun da farko dai hukumar ta bayyana cewa guraban da aka ware na mutum 400,000 ne kacal amma Sai aka samu matasa sama da Milyan 5 da suka cika Fom din neman aikin N-Power din.
Sai dai kuma duk da samun dandazon masu neman aikin, hukumar ta kara makonni biyu domin wadanda suka samu matsala wajen cika Fom din a farkon bude shafin su samu su cika.