KORONA: Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin jihar Filato ya kamu

0

Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin jihar Filato Noel Donjur ya shiga cikin jerin wadanda suka kamu da cutar covid-19 a kasar nan.

Donjur ya kamu ne bayan gwajin cutar da gwamnan jihar Simon Lalong ya tilasta a yi wa dukkan kwamishinonin sa, mukarrabai da sauran ma’aikatan fadar gwamnatin jihar ranar 1 ga watan Yuli.

Kwamishinan yada labarai Dan Manjang ya Sanar da haka wa manema labarai a garin Jos ranar Juma’a.

Manjang ya ce an killace Donjur a daya daga cikin asibitocin Kula da masu fama da cutar a jihar sannan ma’aikatan kiwon lafiya sun fara gudanar da bincike domin gano wadanda ka iya kamuwa da cutar a dalilin yin cudanya da Donjur.

Kwamishinan ya Yi Kira ga mutane da su je asibiti domin yin gwajin cutar a duk lokacin da suka ji rashin lafiya a jikin su.

Gwamna Laling ya gargadi mutanen a jihar da su juri bin dokokin kare kaivdaga kamuwa da cutar korona a domin kauce wa fadawa cikin hadarin kamuwa da ita.

Mutum 393 sun kamu, mutum 164 na asibiti, 219 sun warke sannan 10 sun mutu a jihar Filato.

A Najeriya kuma sama da mutum 27 ne suka kamu da cutar.

Akalla mutum sama da 600 kuma sun rasu inda sama da mutum 10,000 sun warke.

Share.

game da Author