Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta nahiyar Afrika ACDC ta bayyana cewa rabin mutanen da suka kamu da cutar covid-19 a Nahiyar Afrika sun warke.
Hukumar ta ce tun bayan bullowar cutar a kasar Masar a watan Fabrairu mutum sama da 414, 000 sun kamu sannan mutum 10, 260 sun mutu a Afrika.
Kafin cutar ta yadu an yi hasashen za ta yi wa nahiyar Afrika kamu mai tsanani saboda rashin ingantattun kiwon lafiya da yankin ke fama da shi.
Bisa ga hasashen da ‘Imperial College London’ ta yi ta ce Afrika za ta rasa rayukan mutum 300,000 a dalilin cutar sannan hakan ma saboda tallafin dakile yaduwar cutar da Nahiyar za ta samu ne.
UN Economic Commission for Africa ta ce idan babu tallafi Nahiyar za ta rasa rayukan mutane miliyan 3.3 sannan mutum biliyan 1.2 za su kamu da cutar.
A kasar Amurka da cutar ta yi wa kamu mai tsanani kamun farad daya mutum miliyan uku ne suka kamu da cutar inda daga ciki miliyan daya ne kawai suka warke.
Bisa ga sakamakon da hukumar ACDC ta fitar ranar Juma’a ya nuna cewa mutum 414, 011 ne suka kamu da cutar inda daga ciki 195,729 sun warke.
A yanzu dai yaduwar cutar ya ragu a Nahiyar Afrika amma wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun ce akwai yiwuwar mutane da dama sun kamu da cutar ba tare da an sani ba saboda rashin ingantattun shiri na kiwon lafiya.
Rashin tsaurar yin gwajin cutar Covid-19 a Afrika
Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun ce yaduwar cutar covid-19 ya ragu sannan mutane sun warke saboda zafin rana da yankin ke da shi.
Sai dai darektan ACDC John Nkengasong ya bayyana cewa babu tabbacin ko rana shine dalilin warkewar mutane daga cutar covid-19 a Nahiyar Afrika.
Babban mataki dakile yaduwar cutar covid-19 da kasashen duniya suka dauka shine yi wa mutane gwajin cutar sai dai haka bai yi tasiri ba a kasashen Afrika ba.
Kasashen duniya sun yi hasashen cewa cutar zata ci gaba da yaduwa a Nahiyar Afrika daga nan zuwa shida saboda karancin Yi wa mutane gwajin cutar.
Najeriya da ta fi kowace kasa a Afrika yawan mutane na da wuraren yin gwajin cutar guda 40 ne kacal.
Discussion about this post