Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya dakatar da sarkin Misau, maimartaba Ahmed Suleiman da wasu sarakuna biyu a dalilin rikicin gona da ya auku tsakanin Makiyaya da Manoma a yankin Misau.
Sarakunan da aka dakatar sun hada da
Hakimin Chiroma, Yusuf Atiku da Dagacin Zadawa, Bappa Ahmed.
Bayan haka gwamna Bala ya bayyana cewa sarakan za su ci gaba da zama a garin Misau har sai an kammala bincike akan musabban tashin wannan hankali davyayi hasarar rayukan mutane har 9 sannan da dama sun rasu.
Kwamitin zata binciki musabbabin wannan tasgin hankali sannan kuma da bin diddigin matsalolin da ya dabaibaye masu mallakin filaye a wannan yanki.
” Sarakunan za su cigaba da zama a garin Misau amma ba a matsayin sarakai ba domin ba kwamitin damar yin bincuke yadda ya kamata batare da an yi musu katsalandan ba.