KORONA: Kungiyoyin bada tallafi sun horas da ma’aikatan lafiya a Abuja

0

Kungiyoyin ‘Rotary Club da JHPIEGO, sun horas da ma’aikatan lafiya da suka zabo daga cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko 20 dake Abuja.

An zabo wadannan ma’aikatan lafiya ne daga cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake Sauka, Kuchingoro, Lugbe, Tunga-Maje da Bwari.

Kungiyoyin sun horar da ma’aikatan Kan hanyoyin Kare kansu daga kamuwa da cutar covid-19, yadda za su iya dakile yaduwar cutar a tsakanin al’muma sannan da yadda za su inganta kiwon lafiyar Mata da Yara kanana a kasar nan.

Bayan haka kungiyoyin sun raba wa wadannan ma’aikatan kiwon lafiya kayan Kare ma’aikacin lafiya daga kamuwa da cutar sannan da sauran kayan aiki da za su bukata wajen yaki da cutar covid-19 a kasar nan.

Kungiyoyin sun ce sun yi haka ne domin mara wa gwamnati baya bisa kokarin dakile yaduwar cutar Covid-19 da take yi.

Horas da ma’aikatan lafiya ya biyo bayan kukan rashin isassun kayan Kare ma’aikacin lafiya daga kamuwa da cutar da ma’aikatan lafiya ke yi.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO a nahiyar Afrika ta bayyana cewa akalla ma’aikatan lafiya 10,000 ne suka kamu da cutar covid-19 a Nahiyar.

Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce ma’aikatan lafiya 812 ne suka kamu da cutar a Najeriya.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar 26 ga Yuli ya nuna cewa mutum 40,532 ne suka kamu da cutar a Najeriya.

Daga ciki an sallami 17,374 sannan 858 sun mutu.

Sai da babu tabbacin adadin yawan ma’aikatan lafiyan da suka kamu da yawan da suka mutu a kasar nan.

Inganta kiwon lafiyar Mata da Yara kanana

Jami’in kungiyar JHPIEGO Oluwatobi Adebayo, ya koka da yawan matan dake rasa rayukan su wajen haihuwa da rashin amfani da dabaran bada tazarar haihuwa da ake fama da shi a kasar nan.

Adebayo ya ce kasa za ta ci gaba ne idan gwamnati ta maida hankali wajen inganta kiwon lafiyar Mata da Yara kanana.

Mataimakin shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya aa matakin farko dake Abuja Ndaeyo Iwot ya jinjina kokarin da kungiyar Rotary Club ke yi wajen inganta kiwon lafiyar Mata da Yara kanana a kasar nan.

Ya Yi Kira ga gwamnatin tarayya da jihohi da su kafa dokar tabaci a fannin kiwon lafiyar Mata da Yara kanana domin rage yawan Yara da mata da kasarn ke rasawa.

Share.

game da Author