Yadda Ganduje ya maida hakiman da Sarki Ado da Sanusi suka kora, zai maida su masu nada sarakuna a Kano

0

Gwamna Abdullahi Ganduje na so Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gyara dokar jihar ta 2019, yadda zai tabbatar da nadin wasu manyan mukarraban masarautar Kano biyu da marigayi Sarki Ado Bayero da Sarki Sanusi suka sallama, ta yadda za dokar jihar zata tabbatar da nadin su a matsayin manyan hakimai masu nada Sarki a Kano.

Kakakin Majalisar Kano, Abdullahi Gafasa ne ya karanta bukatar Ganduje a gaban zauren majalisa, kuma ana sa ran za su yi zaman tattauna batun kafin karshen watan Yuli.

Hakiman da aka dawo da su masarautar Kano su ne Aminu Babba Dan’Agundi da kuma, wanda ya yi Sarkin Dawaki Mai Tuta da kuma Ciroman Kano, Sanusi Ado-Bayero.

Su biyun dai Sarki Ado da Sarki Muhammadu Sanusi ne suka cire su, bisa zargin yin makarkashiya.

Babba Dan’Agundi ya kalubalanci tsige shi a kotu. Shekaru 17 ana tafka shari’a har dai Kotun Koli ta zartas da cewa ya tsigu.

Shi ne kuma Ganduje ke son ya maida a kan sarautar sa, kuma a gyara doka ya kasance ya na cikin masu nada sarki a masarautar Kano.

Ado Bayero ya cire Dan’Agundi cikin 2003 bayan an same shi da laifin makarkashiya da kuma yin kane-kane cikin lamarin siyasa.

An kafa kwamitin da zai bincike shi, amma aka gayyace shi ya ki zuwa gaban kwamiti domin ya kare kan sa.

Daga nan ya kalubalanci cire shi a Babbar Kotun Jihar Kano har zuwa Kotun Koli.

Kafin Kotun Koli, Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta yanke hukuncin a mayar da Aminu Babba a kan kujerar sa. Amma masarautar Kano karkashin mulkin Muhamamdu Sanunmsi II, ta daukaka kara, inda Kotun Koli ta jaddada cirewar da aka yi masa a matsayin Hakimin Gabasawa, kuma Sarkin Dawaki Mai Tuta, a ranar 5 Ga Yuni.

Bayan an cire Sanusi Bayero, Ciroman Kano saboda ya ki amincewa da Sarautar Ssrkin Kano da aka nada Muhammdu Sanusi II a cikin Yuni, 2014.

Daga baya an nada shi Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa ta Kasa a zamanin Jonathan.

Shi ne aka nada Wamban Kano, a karkashin Sarkin Kano na yanzu.

Share.

game da Author