Yadda sinadarin hana abinci lalacewa ke cutar da kiwon lafiyar mutane a Najeriya – Masana

0

Wasu masana kimiya sun gargadi mutane da su guji cin abincin da da aka yi amfani da sinadarin hana abinci lalacewa cewa cin abinci irin haka na cutar da kiwon lafiyar mutum.

Masanan sun yi wannan gargadi ne bayan binciken da suka gudanar kan ingancin abincin da ake ci a kasar nan.

Sakamakon binciken ya nuna cewa akwai wasu abinci da ake zuba musu sinadari domin hana su rubewa.

Binciken ya kuma nuna cewa an fi amfani da wannan sinadari a wake, garin alabo da busasshhen kifi da ake saida wa jama’a.

Ana amfani da sinadarin ne domin idan mutum ya gani zai yi sha’awar siya yayi amfani da shi.

Sannan cin abinci dake dauke da wannan sinadari na haddasa cutar daji, ciwon koda, bugawar zuciya da sauran su.

An yi kira ga mutanen kasar nan su maida hankali wajen kiyayewa daga amfani da ire-iren wadannan kayan abinci domin kiwon lafiyar su.

Idan ba a manta ba wata kwararriya masaniyar Ingancin abinci Grace Olasumbo ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji cin kayan itatuwan da aka nika su da sinadarin Calcium Carbide.

Olasumbo ta bayyana cewa Sindarin Calcium Carbide sinadari ne mafi yawan ‘yan kasuwa ke amfani da shi wajen nika danyen kayan itatuwa, wato kayan marmari.

Bincike ya nuna cewa gajartan hakuri da hadama na cikin abubuwan da ke sa ‘yan kasuwa yin amfani da wannan sinadarin domin a cikin kwana daya yake nunar da kayan itatuwa.

Olasumbo ta bayyana cewa wani abin da ‘yan kasuwa suka kasa ganewa shine amfani da wannan sinadarin don nunar da kayan marmari na yi wa kiwon lafiyar mutane illa matuka.

A dalilin haka akan kamu da cututtuka da suka hada da amai da zawo, ciwon ido, gyambon ciki, dajin makogwaro, baki, hanta da sauran su.

Share.

game da Author