Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ta bada umarnin cewa a gaggauta mayar wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki dukkan gidahen sa biyu da Hukumar EFCC ta kwace masa.
Mai Shari’a Rilwanu Aikawa ya ce EFCC ta kasa gabatar da kwararan dalilan da kotu za ta gamsu da halascin kwace gidajen dindindin daga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Saraki.
Cikin watan Disamba ne dai akkalin ya bada umarnin kwace gidajen, amma kwacewar wucin-gadi, ta wani lokaci kawai ba dindindin ba.
Gidajen guda biyu dai sun hada da wadanda ke lamba 10 da na 11, Abdulkadir Road, GRA, Ilorin.
EFCC ta shaida wa kotu cewa Saraki ya sayi gidan ta hanyar cuwa-cuwa, a lokacin da ya ke gwamnan jihar Kwara.
EFCC a lokacin ta shaida wa kotu cewa akwai wani mummunan rahoto na sirri da ya nuna irin harkalla, tabargaza da wandaka da kudade da Saraki ya tabka, a lokacin ya na gwamnan jihar Kwara tsakanin 2003 zuwa 2011.
Aikawa ya ki amincewa da kwace gidajen dindindin, saboda rashin gamsasshiyar hujja daga EFCC.
Don haka ya bada umarnin a maida masa gidan sa kawai.
Ssraki ya yi ta kai gwauro ya na kai mari a kotu, ya na kai karar EFCC, cewa ta kwace masa gida ne kawai saboda bi-ta-da-kullin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi masa.