Yanzu dai EFCC tilas ta kyale ni haka nan, na rika walwala ta kamar kowa -Saraki, bayan hukuncin kotu

0

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, ya bayyana cewa yanzu dai tilas din Hukumar EFCC ta hakura, ta kyale shi ya sarara haka nan, kamar kowane dan Najeriya.

Saraki ya yi wannan kakkausan furuci ne bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos ta umarci EFCC ta sakar masa gidajen sa biyu da ta kwace tun tsawon shekarun baya.

Saraki a ranar Juma’a din nan ya ce ya na farin ciki da wannan hukunci, saboda kotu ta ce EFCC ta kasa gabatar da hujjojin cewa da kudin sata Saraki ya sayi gidajen, a lokacin ya na gwamna.

Ya ce shekaru biyar baya har zuwa yau, ya shiga cikin kalubale masu tsaurin gaske. Ba ma shi kadai ba, har da iyalin sa.

“Na yi juriyar fafata yaki kuma ina yin nasara tsakani na da wannan karyar ko da wancan sharri ko wadancan tuggu zuwa wasu.

“Kuma duk ba wata aba ba shi sai kutunguilar kitsa min kulle-kullen cusa min fargaba da barazana ta hanyar ci min mutunci, ci min fuska da sharrin wawurar kudade na karya. To na gode Allah da ya dora ni akan mashararranta.”

Ya kuma yi zargin cewa EFCC a karkashin Magu ya dauki batun kin tantance shi da Majalisar Dattawa ta yi, ya maida batun ya zama gaba da ‘yar-,tsama tsakanin Magu da Saraki din.

“Ni kuwa na san kin tantance Magu ya zama cikakken Shugaban EFCC da muka yi, a bisa ka’idar da dokar kasa ta gindaya mu ka yi. Saboda ba mu wa wata hamayya ko kiyayya ga Magu.

“Don haka la’akari da hukuncin da kotu ta yanke a yau, ya kamata EFCC ta sani cewa yaki da cin rashawa ba abu ne da za a maida harin bi-ta-da-kulli da kokarin cimma wata boyayyar manufar wata kitimirmira ba.”

Ya yi kira ga EFCC ta dauki darasi daga yau da kuma shari’ar da Sarakin ya ce ya tabka shi da Hukumar CCT inda ya tandara hukumar da kasa a Kotun Koli.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Kotun Tarayya ta ce a maida wa Saraki gidajen ta da EFCC ta kwace

Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ta bada umarnin cewa a gaggauta mayar wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki dukkan gidahen sa biyu da Hukumar EFCC ta kwace masa.

Mai Shari’a Rilwanu Aikawa ya ce EFCC ta kasa gabatar da kwararan dalilan da kotu za ta gamsu da halascin kwace gidajen dindindin daga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Saraki.

Cikin watan Disamba ne dai akkalin ya bada umarnin kwace gidajen, amma kwacewar wucin-gadi, ta wani lokaci kawai ba dindindin ba.

Gidajen guda biyu dai sun hada da wadanda ke lamba 10 da na 11, Abdulkadir Road, GRA, Ilorin.

EFCC ta shaida wa kotu cewa Saraki ya sayi gidan ta hanyar cuwa-cuwa, a lokacin da ya ke gwamnan jihar Kwara.

EFCC a lokacin ta shaida wa kotu cewa akwai wani mummunan rahoto na sirri da ya nuna irin harkalla, tabargaza da wandaka da kudade da Saraki ya tabka, a lokacin ya na gwamnan jihar Kwara tsakanin 2003 zuwa 2011.

Aikawa ya ki amincewa da kwace gidajen dindindin, saboda rashin gamsasshiyar hujja daga EFCC.

Don haka ya bada umarnin a maida masa gidan sa kawai.

Ssraki ya yi ta kai gwauro ya na kai mari a kotu, ya na kai karar EFCC, cewa ta kwace masa gida ne kawai saboda bi-ta-da-kullin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi masa.

Share.

game da Author