Aikin rabon maganin sauro ga mata masu ciki da kananan yara wato shirin za’a Jefi tsuntsu 2 da Dutse 1 (SMC/ MNCHW)
Hakika shirin da Gwamnatin Jahar Kano ke gabatarwa domin dakile zazzabin cizon sauro da kuma yunkuri dakile mace macen mata masu ciki da kananan yara musamman a wannan lokacin na damina abin ayaba ne
Gwamnatin Jahar Kano Karkashin Jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje tayi abinda ake kira farar dabara ce wato shiga rijiya da fura.
Koda da ba’a gabar da aka gama kullen zaman gida dole, kasancewar mata na cikin shirin zai bunkasa tattalin arziki kasancewar kafatanin jahar Kano aka dauko matan kuma dama mata sun Dade suna hangen samun wasu shirye shirye da zasu samu aiyukanyi da jari shine abinda zai farfado da tattalin arziki duba da Cewar sune masu kananan sana’oi acikin unguwa kuma sune ahakku wajen bunkasa su.
Matan da ke sana’ar saida:
– kuli da Mangyada
– koko da kosai
– Danwake
– kayan miya
– Waina
– Sana’ar Abinci
Da sairansu sun shiga shirin rabon maganin bayan karbar horo
A mahangata wannan shirin bayan dakile zazzabin cizon sauro Zai dakile masassara tattalin arzikin da corona virus ta jefa Mata saboda kullen zaman gida jarinsu yayi kasa.
Mafita, mazaunin garin Kano ne, a Unguwar Sharada.
Discussion about this post