Hadaddiyar Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta bayyana cewa ba lallai ba ne a sake bude Jami’o’i ko da kuwa Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin a sake bude makarantun kasar nan.
Shugaban ASUU na kasa baki daya, Biodun Ogunyemi ne ya bayyana haka, a wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES ta wayar tarho a ranar Lahadi din nan.
Sannan kuma ya kara yin cikakken bayani kan matsayin sa dangane da kiran da ASUU ta yi cewa kada Gwamnatin Tarayya ta sake bude makarantu sai cikin 2021.
Gwamnatin Tarayya ta rufe dukkan makarantun firamare, sakandare, na gaba da sakarandare da jami’o’in kasar nan a ranar 29 Ga Maris, bayan barkewar cutar Coronavirus a Najeriya.
Kwana kadan bayan rufe makarantu kuma sai malaman jami’o’i suka shiga yajin aikin da har yau ba su hakura ba.
Malaman sun tafi yajin aikin saboda nuna rashin amincewa kan yadda aka rike wa dama a cikin malaman kudaden albashin su, saboda sun ki yin ranista da tsarin biyan albashi na gar-da-gar, wato IPPIS.
Yayin da gwamnati ta fitar da ka’idojin da makarantu za su cike kafin a sake bude makarantu domin masu jarabawar fita sakandare, babu abin da gwamnati ta shirya wa jami’o’in kasar nan.
Ogunyemi ya kara da cewa, “mu ba mu ce kada a koma makaranta ba sai nan da 2021 ba. Mun dai ce a duk lokacin da gwamnati ta ga cewa lafiya kalau babu wata barazanar da cutar Coronavirus za a iya fuskan”.
Ya ce tilas gwamnati ta tabbatar cewa makarantu sun cika sharuddan da gwamnati ta gindaya kafin a fara komawa makarantu.
Ya ce akwai matsaloli jingim a Jami’o’i. Saboda ba za ka cimma farfagandar yin nesa-nesa da juna ba, alhali ba a gina wadatattun ajujuwan da dalibai za su iya zama ba su gwamutsu da juna ba.
Discussion about this post