Dakarun sojin Najeriya dake aikin ‘Operation WHIRL STROKE’ sun ceto Mutum 34 da aka yi garkuwa da su sannan sun sun kwato makamai da dama a jihar Benuwai.
Kodinatan yada labarai na rundunar sojin Najeriya, John Enenche ya fadi haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Juma’a a Abuja.
Enenche ya ce rundunar ta yi nasarar ragargaza wadannan maharan ne bayan samun bayanan sirri na ayyukan su.
Ya ce a ranar 16 ga watan Yuli dakarun sun farwa mabuyar mahara dake kauyen Tomayin inda Suka kashe shugabannin kungiyoyin wanda a ciki akwai wani gogarma mai suna Zwa Ikyegh sannan sauran mabiyan kungiyar sun gudu da raunin harsashi a jikin su.
Dakarun sojojin sun kwato bindigar AK 47 guda daya, kananan bindigogi guda bakwai, harsashen bindiga, babura biyu da layuka dabam-dabam.
Enenche ya ce sojoji sun kama Sealemun da Orduem da ake zarginsu da yin garkuwa da mutane a kauyen Austoma dake karamar hukumar Ukum.
Ya ce an Kama wadannan mutane da babur na hawa guda daya da suke amfani da shi wajen aikata muggan aiyukkan su.
Enenche ya ce dakarun sojojin na tsare da su sannan da zaran sun kammala bincike a kan su za su danka su hannu ‘yan sanda.
Discussion about this post