JA YA FADO JAJAYE SUN KWASHE: Yadda EFCC ta yi wa Fadar Buhari da Ma’aikatun Gwamnati watandar wasu kayan da ta kwato daga hannun barayin gwamnati

0

Hukumar EFCC ta raba wasu kayan da ta kwato zuwa Fadar Shugaban Kasa da kuma wasu Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, maimakon ta yi gwanjon kayan, kuma ta zuba kudaden cikin Asusun Gwamnatin Tarayya a Babban Bankin Najeriya, kamar yadda dokar da ta kafa EFCC ta bayyana.

Bayanin yin watandar wadannan kayayyaki na cikin bayanin da Ibrahim Magu dakataccen shugaban EFCC ya yi wa Kwamitin Bincike, inda ya ke kare kan sa daga zargin ya azurta kan sa da kayan da hukumar ta kwato daga hannun barayin gwamnati.

Dokar EFCC dai ta fayyace cewa duk kayan da aka kwato daga barayin gwamnati, to a yi gwanjon su kuma a ajiye kudin a Asusun Gwamnatin Tarayya, sannan a raba kudaden tsakanin Gwamnatin Tarayya, Gwamnonin Jihohi da Gwamnatocin Kananan Hukumomi, a yi wa jama’a ayyukan raya kasa da kudaden.

Wasikar da Magu ya rubuta wa Shugaban Kwamitin Bincike Ayo Salami, ta fado hannun PREMIUM TIMES, kuma ya ce zargin da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya yi masa wai ya yi wa kayan da ya kwato a hannun barayin gwamnati sata-ta-saci-sata, karya ce, kuma kazafi da sharri ne domin a zubar masa da kima kawai.

“Daga lokacin da na hau shugabancin EFCC har zuwa yau, ko sau daya ban taba azurta kai na da kayan da na kwato daga hannun barayin gwamnati ba. Ban yi gwanjon ko abu daya na danne kudin ba.” Inji Magu.

Ya ce duk kayan da ya kwato wa gwamnati na nan daram, sai fa wadanda ya raba wa wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya bisa iznin ofishin shugaban kasa.

Dalla-dallar Watandar Da EFCC Ta Yi Da Bisa Umarnin Ofishin Shugaban Kasa:

Ya ce daga cikin kayan da ya kwato, kudin gwanjon wasu taraktoci 244 ne kacal ke cikin Asusun Bai Daya na Gwamnatin Tarayya da ke CBN.

Magu ya ce kayayyakin da aka yi watanda bisa unarnin Shugaba Muhammadu Buhari, sun hada da motocin da aka raba wa Ma’aikatar Ayyukan Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma.

Magu ya ce an cire kudaden motocin daga kudaden da gwamnatin tarayya ke bai wa Ma’aikatar.

Sannan kuma ya yi ikirarin cewa an raba wasu motocin ga Fadar Shugaban Kasa, Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira, Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta Kasa (FIRS) duk sun kwashi rabon na su motocin.

Ya kara da cewa akwai baburan da aka raba wa Hukumar Samar da Ayyuka ta Kasa (NDE).

Sauran Wadanda Suka Kwashi Kason Watandar Kadarorin:

Ma’aikatu da Hukumomin da aka yi wa watandar kantama kantaman gidaje, ofisoshi da rukunin gidaje sun hada da Muryar Najeriya (VON), NDE, Ma’aikatar Ayyukan Jinkai, Ma’aikatar Raya Yankin Arewa maso Gabas da kuma Hukumar Saisaita Tsarin Fansho ta Kasa (PTAD).

EFCC kuma ta raba wasu kadarorin da aka rike a matsayin wucin-gadi ga Rundunar Sojojin Najeriya, Ma’aikatar Kudade ta Kasa, Hukumar Kula da Kudade ta Kasa (FRC), Hukumar Kula da Harkokin ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje da kuma Hukumar Kula da Filayen Jiragen Saman Najeriya (FAAN).

Magu ya ce wadannan duk haya aka ba su suka kama. Amma bai bayyana hukuma ko ma’aikatar da aka bai wa kudaden hayar ba.

Sannan Magu ya ce EFCC ta amince Gwannatin Jihar Lagos ta yi amfani da wani gini da hukumar ta kwace a Lagos, cewa ta yi amfani da shi a matsayin wurin killace masu cutar Coronavirus. Ginin dai kwacewar wucin-gadi ce kotu ta bayar da umarni aka yi masa. Ba a kai ga kwace shi dindindin ya zama mallakar gwamnatin Najeriya ba.

Ya kara da cewa ya samu umarni daga gwamnatin tarayya ya yi gwanjon wasu motoci sama da 450 da aka kwace a Abuja da Lagos. Kuma har Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje tare da Hukumar Kula da Motocin Gwamnati sun yi wa motocin sama da 450 kudin-goro.

Share.

game da Author