‘Yan bindiga sun kashe Fulani makiyaya uku a Kaduna

0

‘Yan bindiga sun kashe wasu Fulani majiya a kauyen Fari dake Karamar Hukumar Kauru, a jihar Kaduna.

Wadannan makiyaya sun gamu da ajalin su ne bayan wasu ‘yan bindiga daga Karamar Hukumar Zangon Kataf sun Yi tattaki har kauyensu suka kashe su.

Wadanda aka kashe akwai Muhajid Musa Mai shekaru 7, Sanusi Ayuba, mai shekaru 10 sai kuma Abashe mai shekaru 30.

” Wani jami’in tsaro da baya so a fadi sunan sa ya shaida cewa kisar ramuwar gayyace.

A Cikin hotunan da ka nuna na wadanda aka kashe, daya daga Cikin su ma yankar rago aka yi masa.

Kwamishinan ‘yan sandan Kaduna Mohammed Ajile bai ce komai ba game da harin ko da PREMIUM TIMES ta nemi ya ce wani abi akai.

Dalilin da ya sa rikicin kudancin Kaduna yaki ci yaki cinyewa – Fadar Shugaban kasa

Fadar shugaban Kasa ya bayyana cewa dalilin da ya sa zaman lafiya ya gagara tabbata a yankin kudancin Kaduna shine yadda aka maida ta’addanci wani salo na siyasa, kashe-kashe ta hanyar kabilanci da ramuwar gayya a tsakanin mutane.

Rayukan daruruwan mutane sun salwata a dalilin hare-haren ta’addanci a yankin a shekarun da suka wuce. Irin wannan kashe-kashe yayi tsani duk da jibge dakarun sojoji da gwamnatin tarayya ta yi a yankin.

” Ba kamar wasu yankunan kasar nan dake fama da hare-haren ta’addanci ba, salon na yankin kudancin Kaduna da bam yake.

” Ya tabbata daga bayannan dake kasa cewa kashe-kashen yankin kudancin Kaduna ya karkata ne ga yadda aka maida ta’addanci wani salo na siyasa, kashe-kashe ta hanyar danganta rikici da kabilanci ko addini da ramuwar gayya a tsakanin mutane.

” Wani dan ta’adda zai farwa irin sa dake ba kabila ko addinin su daya ba. Hakan sai a dauka kuma su a bangaren da aka kashe suma su far wa wadancan bangaren, sai kuma a jefa addini da kabilanci a ciki. Wannan ya kai hari, daga baya wancan bangaren suma su dau fansa.

Akarshe fadar gwamnati ta hori jama’a da su daina daukar doka a hannun su. Maimakon haka su rika sanar da jami’an tsaro dake jibge a wannan yanki.

Fadar gwamnatin Buhari ta jajanta wa mutanen yankin da aka kashe a harin kwana-kwanan nan a Igali, Birnin Gwari da Giwa.

Share.

game da Author