Dangiwa Umar, Shehu Sani da Agbakoba sun musanta shiga wata sabuwar siyasa

0

Wasu fitattun ‘yan Najeriya uku, tsohon gwamnan soja, Kanar Dangiwa Umar, Sanata Shehu Sani da Lauya Olisa Agbakoba sun musanta cewa su na cikin mambobin sabuwar tafiyar siyasar da ta bayyana a cikin wannan makon.

Sun ce su ukun da sunayen su suka bayyana a cikin jadawalin wadanda aka ce su ne jiga-jigan tafiya, duk an tsarma sunayen ne ba tare da an ji ra’ayin su, ko an nemi amincewar su ba.

Yayin da Umar da Shehu Sani suka nesanta kan su da sabuwar tafiyar ta hanyar tattaunawa da PREMIUM TIMES, shi kuma Agbakoba sanarwa ya fitar, inda shi ma ya nesanta kan sa.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda wata tawagar jiga-jigan ‘yan Najeriya da suka hada da ‘yan kashe hakki, kwararru, masana, suka kafa rundunar siyasa mai shirin narkewa ta koma jam’iyya domin tunkarar zaben 2023.

Wani mai suna Anthony Kila ne ya yi sanarwar bayyanar sabuwar tafiyar, cikin wata takardar sanarwar da ya tut-tura wa gidajen jaridu.

Kila ya ce an kirkiro sabuwar tafiyar ce bayan shafe wata guda cur ana tuntubar juna da gudanar taron kowa-daga-nesa.

Cikin wasu da aka lissafa a tafiyar har da Ghali Na-Abba, Obadiah Mailafia, Femi Falana, Oby Ezekwesili, Jibrin Ibrahim, Chidi Odinkalu, Isa Aremu da sauran su.Dangiwa Umar, Shehu Sani da Agbakoba sun musanta shiga wata sabuwar rundunar siyasa

Share.

game da Author