Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da gaggauta dakatar da Shugaban Hukumar Zuba Jarin Kudaden Inshora ta NISTF, Adebayo Somefun.
Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka, a cikin wata takarda da Kakakin Yada Labaran Ngige mai suna Charles Akpan ya fitar a ranar Alhamis, ta kuma bayyana sunayen daraktocin da dakatarwar ta shafa.
Sun hada da Jesper Azuatalem, wanda shi ne Babban Daraktan Kudade da Zuba Jari. Sai kuma Olukemi Nelson, Babban Daraktan Gudanarwa.
Sauran sun hada da Tijjani Darazo, Olusegun Bashorun, Lawan Tahir Chris Esedebe, Olodotun Adegbite, Emmanuel Enyinnaya.
Akwai kuma Olutoyin Arokoyo, Dorathy Zajeme-Tukura da Victoria Ayantuga.
Minista Ngige ya ce dakatarwar da aka yi musu ta samo asali ne daga wata karma-karma da asarkalar makudan kudaden kwangiloli ne da binciken farko ya fara ganowa cewa an tafka.
“A wannan lokacin dakatarwar, dukkan su za su fuskanci kwamitin bincike domin bibiyar yadda aka rika bayar da kwangiloli a hukumar, tun daga 2016 har zuwa yau.
“Asarkalar da aka rika tafkawa a NSITF ta jefa gudummawar masu zuba jari a cikin hukumar shiga halin tsaka-mai-wuya.
“An kuma umarci wadanda aka dakatar din bayar damka ayyukan ofisoshin su a hannun na kasa da su ga girma.
An umarci Kelly Nwagha ya karbi ragamar rikon hukumar na wucin-gadi.
Sanarwar ta ce wadanda aka damka wa rikon hukumar za su fara aikin rikon daga ranar 6 Ga Yuli, 2020 har zuwa yadda hali ya kama.
An umarci Shugaban Hukumar Gudanarwar Hukumar ya tabbatar Kwamitin Bincike ya fara aiki da gaggawa.
An kuma gargadi wadanda aka ba rikon-kwarya cewa kada su ci amanar dukiyar kudaden dimbin jama’ar da aka damka musu.
Discussion about this post