BABBAN SALLAH: Buhari zai yi Sallar Idi a fadar Shugaban Kasa, ba zai yi maraba da baki ba

0

Fadar shugaban kasa ta sanar cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi sallar idi a gida ne kuma ba zai yi maraba da baki ba.

Garba Shehu da ya fitar da wannan sanarwa ya bayyana cewa, shugaba Buhari yayi haka ne domin bin shawarwarin Majalisar Koli na Addinin Musulunci, NSCIA da kuma kwamitin Shugaban kasa kan dakile yaduwar Korona suka bashi.

Bayan haka ya ce babu ziyarar gaisuwa na ko ‘yan siyasa da sauransu a lokacin da ake shagulgulan sallar.

Akarshe ya hori yan Najeriya da su tabbata sun kiyaye dokokin da aka sanar don Korona.

” Idan za ayi Sallah a masallaci, a saka takunkumin fuska, sannan a bada tazara a tsakanin juna.

Share.

game da Author