Ma’aikatar Ilimi ta bayyana ranakun da daliban ajin Karshe za su rubuta jarabawar kammala karatu.
Ma’aikatar ta fidda jadawalin ranakun da za a rubuta jarabawar karshe na daliban ajin karshe ranar Laraba in da ta shaida cewa gaba daya kaf za a kammala jarabawa a makarantun kasar nan a watan Nuwamba.
Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajuiba ya sanar da haka bayan ya kammala zama da shugabannin hukumomin jarabawar ajin karshe da ya yi a Abuja.
Ga yadda aka tsara:
1. Za a fara rubuta jarabawar NABTEB ranar 21 ga Satumba a kammala ranar 15 Oktoba.
2. Jarabawar NECO da yan ajin karshe na babban sakandare ke zanawa za gudana ne daga ranar 5 ga Oktoba zuwa ranar 18 ga Nuwanba.
3. Za a rubuta jarabawar NECO na ‘yan ajin karshe na karamar Sakandare JSS 3 ranar 24 ga Agusta sannan a kammala ranar 7 ga Satumba.
4. Jarabawar shiga makarantun sakandare da ‘yan aji shida na makarantun firamare ke rubutawa wato NCEE za a rubuta ranar 17 ga Oktoba na 2020.
5. Za a kammala rajistan jarabawar NECO da ake yi yanzu rana 10 ga watan Satumba 2020 sannan ma’aikatar ilimi ta ce ba za a kara kwanaki ba.
6. Za a rubuta jarabawar NBAIS ranar 23 ga Satumba a kammala ranar 17 ga Oktoba.
Ministan ilimi Nwajuiba ya umurci duk hukumomin rubuta jarabawar da su gaggauta fidda jadawalin Jarabawar su nan da mako daya.
Ya kuma ce dole ne dalibai su zo wurin rubuta jarabawar da takunkumin fuska da man tsaftace hannu.