Sabbin dokokin shiga masallatai da Coci-Coci 8 da hukumar NCDC ta fitar

0

A ranar Lahadi, hukumar Dakile yaduwar cututtuka ta Kasa NCDC, ta fidda sabbin dokokin da masallatai da Coci-Coci za su tabbatar an bi kafin a shiga wurin yin Ibada.

Hukumar ta ce a dalilin sassauta doka da ake yi domin kyale mutane su ci gaba da hidimomin su gami da zuwa wuraren ibada ta tsara sabbin dokoki da dole a lokacin da za a shiga masallaci ko coci.

Ga dokokin:

1 – Dole ko kai waye harda liman da ladan, kowa sai ya saka takunkumin fuska idan zai shiga masallaci ko coci.

2 – Duk wanda bashi da lafiya ya hakura da zuwa masallaci ko Coci. Sannan kuma a tabbata samar da na’aurar gwajin yanayin jikin mutum.

3 – A samar da bukitin ruwa da sabulu, sannan a jingine man tsafatce hannaye a wuraren shiga da lungunan masallaci da Coci.

4 – Wadanda za su shiga wuaren Ibada kada su wuce mutum akalla daya bisa uku na yawan mutanen da dakin zai dauka.

5 – A tsara yadda za a zauna saboda a bada tazarar akalla mita biyu tsakanin mutane dake wurin ibada.

6 – A yi nesa-nesa da juna ko da bayan an kammala ibada, kamar yin musabaha da juna.

7 – A rage yin abinda zai sa a rika kusantar juna. Yana da kyau mutum yi alwalarsa tun daga gida.

8 – A rika yi wa wuraren ibada feshin kashe kwayoyin cuta akai-akai.

Share.

game da Author