Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal yayi kira ga majalisar Kasa ta kirkiro dokar da zai sa a yanke wa wanda ya mallaki makami ba tare da lasisi ba hukuncin kisa ko kuma a daure shi a gidan kaso na tsawon rayuwar sa.
Tambuwal ya fadi hakane da yake tattaunawa da dalibai a garin Sokoto ranar Asabar wanda kakakin sa Muhammad Bello ya fitar.
Gwamna Tambuwal ya ce akwai makamai kanana da manya a hannun miutane da dama a kasar nan fiye da wadanda ke hannun jami’an tsaro.
” Ina kira ga gwamnati majalisar kasa da fadar shugaban Kasa da su hadu a kirkiro wata kudiri da zai zama doka domin hukunta duk wanda ya mallaki makami ba tare da lasisi ba.
” Duk wanda ya ke da makami ya je ayi masa rajista, idan kuma babu halin yi mata rajista ya tattara su ya mika wa gwamnati. Ya ce idan za a yi haka sai a ba mutane lokaci su yi haka. Idan mutum bai yi ba sai a hukunta shi kai tsaye.
Sannan haka yayi kira ga gwamnati da ta inganta albashi da jin dadin jam’an tsaron kasar nan.
Bayan haka gwamnatin jihar karkashin shugabacin gwamna Aminu Tambuwal, na tsara wani shiri da za tai kafa kungiyoyin ‘yan banga, da za a tura yankunan jihar domin samar da tsaro a jihar.