KORONA: Mara lafiya daya tal ya rage mana a Jigawa, mun sallami duka mutum 307 da ke killace

0

Gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru ya bayyana cewa gwamnati ta sallami duka mutum 307 da aka killace saboda cutar Korona.

” An sallami mutum 307 da ke killace ana basu magani saboda kanuwa da suka yi da Korona. Mutum 9 sun mutu, saura mana mutum daya tal, da ke asibiti bai warke ba.

Gwamna Badaru ya fadi haka a jawabin sa a wajen taron manema labarai, a garin Dutse.

Bayan haka kuma gwamnati ta bude duka iyaykokin ta da wasu jihohin kasarnan da ta garkane tun a watan Maris sannan kuma ta sanar da bude kasuwannin mako-mako da ta garkame a baya.

” Muna rokon Allah yasa kada mu sake komawa halin da muka fada a baya da ya kai ga mu dauki wadannan matakai masu tsauri a jihar.

” Sannan kuma muna yi wa Allah godiya da yasa a cikin kwanaki hudu da suka wuce ba a samu rahotan bullar cutar a ko ina ba ko kuma wani dan jihar ya kama.

Sannan kuma gwamna Badaru ya ce an rufe babban sansanin da aka bude domin killacewa da kula da wadanda suka kamu da cutar dake Fanisau har sai an sake samun rahotan wani ya kamu.

Bayan haka ya ce gwamnatin Tarayya ta ba jihar gudunmawar naira biliyan daya da kuma tirelolin buhunan abinci 150 domin tallafawa talakawa a jihar.

Haka zalika gwamna badaru ya ce makarantu za su ci gaba da zama a kulle har sai yanayin yaduwar cutar ta ragu matuka a kasa baki daya.

Share.

game da Author