Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya ce tilas sai an yi taron kasa domin a samo hanyoyin da Gwamnatin Tarayya za ta rage kashe kudade barkatai.
Osinbajo na magana ne a wurin wani taro da ‘Emmanuel Chapter’ ta shirya a ranar Juma’a.
Mataimakin na Buhari ya yarda cewa gwamnati na kashe kudade barkatai ta hanyoyi birjik wadanda za a iya cire su daga dokokin kasar nan, domin a rage kashe kudade a bangarorin da ko ribar sisin kobo ba a samu.
Osinbajo ya yi bayanin ne a kokarin da ya yi wajen amsa tambayar da Sarkin Kano Murabus Muhammadu Sanusi ya yi masa.
Karfen-kafar Hana Kashe Kudade:
Osinbajo ya ce babbar matsalar da ake fuskanta ita ce tilas ‘yan majalisa ne ke da alhakin gyara dokar wuraren da za a rage kashe kudaden.
“To kuma su ne sahun gaba na masu amfana da wadannan makudan kudaden da ake kashewa har ake korafin sun yi yawa.
Sanusi ya yi wa Osinbajo tambaya cewa:
“Ba don kada a ce kuma na raina mutane ba, da sai na ce lokacin rage kashe kudaden gwamnati barkatai ya yi, muddin kasar nan na son ta tsira da mutuncin ta.
Misalin Fifikon Birnin Atlanta da Najeriya:
Sanusi ya ce ga birnin Atlanta nan da ke Amurka, amma abin da ya ke samu daga cinikin ‘tesla’ ya fi karfin kasafin kudin Najeriya na shekara daya. Kuma ba shi ne birni mafi arziki a Amurka ba.
“Ya kamata a rage yawan Majalisar Tarayya da ta Dattawa. Su koma wucin-gadi, yadda sai ranar da suka zauna kadai za a biya su kudin alawus.
Kananan Hukumomi su ma kamata ya yi a maida rikon su a hannun jami’an Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi.” Inji Sanusi Lamido.