Mutum 2 cikin 3 dake neman shiga manyan makarantun kasar nan basu samun adimishon

0

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’in kasar nan ta bayyana cewa mutum biyu cikin mutum uku dake cika fom din shiga manyan makarantun kasar nan ba a dauke ba a shekarar 2019.

Cikin dalibai miliyan biyu da suka nemi shiga jami’o’i da manyan makarantun Najeriya, dalibai 600,000 ne kacal aka iya dauka a manyan makarantun.

Alkaluman bayanan sun nuna cewa dalibai 444,947 suka samu shiga jami’o’in kasar nan.

Dalibai 96,423 suka shiga kwalejojin kimiyya da fasaha dake Najeriya, sai kuma dalibai 69,810, suka shiga makarantun kowan aikin malunta wato kwalejojin Ilimi.

JAMB ta ce dalibai sama da miliyan daya sun sun samu adadin makin da ake buka ta su shiga jami’a kuma sun ci jarabawar kammala makarantar sakandaren kasar nan.

Ba tun yanzu ba ake kukar rashin isassun manyan makarantu a kasa Najeriya da zasu iya daukan yawan dubban daliban da ke kammala karatun sakandare a kasar nan sannan suke neman shiga manyan makarantu.

Duk da kakkafa jami’o’i masu zaman kansu da aka yi a kasar nan dalibai masu dinbin yawa ne ke kasa samun shiga manyan makarantu bayan kammala karatun su na sakandare a kasar nan.

A cikin watan Mayu ma’aikatan ilimin Najeriya ta amince wawasu jami’o’i su rika yin karatun nesa da dalibai wato ( Distance Learning) . Wasu na ganin hakan zai kara yawan dalibai da zasu rika samun daman yin karatun gaba da sakandare a kasar nan.

Share.

game da Author