EFCC ta kwato Naira miliyan 400 a cikin wata shida a shiyyar Sokoto

0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) dake kula da shiyar Sokoto da ya hada da jihohin a Kebbi, Sokoto da Zamfara ta kwato naira miliyan 400 a cikin watannin shida wato daga watan Janairu zuwa 16 ga watan Yuni 2020 daga baragurbin ‘yan Najeriya da suka yi sama da fadi da su.

Shugaban Hukumar dake kuka da wannan shiyya Abdullahi Lawal ya Sanar da haka wa manema labarai a garin Sokoto ranar Laraba.

Lawal ya ce Hukumar ta kuma samu nasarar kama mutum bakwai da suke da hannu a sata ko kuma sama da fadi da kudade a tsakanin wannan lokaci.

Ya kuma ce a cikin watanni 6 hukumar ta saurari kararraki kan harkallar filaye, sama da fadi da kuma almundahada.

Lawal ya kuma ce Hukumar takama wasu shugabannun Kungiyar ‘yan kasauwa dake jihar Sokoto da suka yi sama da fadi da Naira biliyan 1 da gwamnati ta basu bashi amma suka ki dawo da su.

Share.

game da Author