Gwamnati ta tallafa wa manoman masara 535 da kayan aikin noma na Naira miliyan 89

0

Babban bankin Najeriya (CBN) a shirin tallafa wa manema na ‘Anchor Borrowers Programme (ABP)’ ya tallafa wa manoman masara 535 da kayan aikin noma da ya kai Naira miliyan 89 a jihar Anambra.

Shugaban Kungiyar manoman masara na Najeriya (MAAN) reshen jihar Anambra Simeon Nwafor ya Sanar da haka a taron raba wa manoman kayan tallafin da aka yi a garin Onitsha ranar Talata.

Nwafor ya ce adadin yawan manoman da suke amfana da wannan shiri ya karu daga 122 a shekara 2019 zuwa 535 a 2020.

Ya yi kira gwamnati da ta gaggauta raba wa manoma kayan tallafi da wuri ganin cewa bana manoma da dama sun samu shiga cikin wannan shirin.

Nwafor ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban Kungiyar MAAN ta kasa Abubakar Funtua bisa wannan tallafi da suka raba wa manoma a jihar.

Bayan haka raba kudi na bankin CBN Awka Bridget Okparaeze ta ce wannan shine karo na biyu da manoma a jihar ke amfana da Wannan shiri tun tun kafa tsarin a shekaran 2015.

Ta ce gwamnati ta tsara Wannan shiri ne domin inganta aiyukkan noma a kasar nan ta hanyar ganin manoma sun noma abincin da ake ci sannan mutanen kasar nan na cin abinci da suka noma da kan su.

Bridget ta ce gwamnati ta bada wannan tallafi a matsayin bashi ga manoma za su biya bayan kaka.

Share.

game da Author