KORONA: Najeriya ta zarce mutum 21,000 da suka kamu, mutum 533 sun rasu

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 452 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Talata.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 209, Oyo – 67, Delta – 37, Ogun – 36, FCT – 22, Abia – 20, Enugu – 16, Bauchi – 15, Kaduna – 8, Ondo – 8, Osun – 7, Imo – 3, Benue – 3, and Borno 1.

Yanzu mutum 21, 371 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 7, 338 sun warke, 533 sun rasu.

Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum,9, 073, FCT – 1,190, Kano – 1,190, Oyo – 1,055, Rivers – 930, Edo – 797, Ogun – 699, Kaduna – 608, Delta – 569, Bauchi – 482, Gombe – 479, Borno – 477, Katsina – 434, Jigawa – 317, Ebonyi – 264, Plateau – 253, Imo – 246, Abia – 252, Nasarawa – 193, Kwara – 200, Sokoto – 138, Ondo – 162, Bayelsa – 177, Enugu – 160, Zamfara – 76, Kebbi – 67, Osun – 67, Anambra – 66, Niger – 66, Yobe – 56, Osun – 67,Akwa Ibom – 65, Adamawa – 45, Benue – 47, Ekiti – 35, Taraba – 18, Taraba – 18, and Kogi – 3.

Hukumar NCDC ta gargadi mutane da su kula da tsoffi musamman wadanda ke fama da rashin lafiya kamar Asma, ciwon siga da dai sauran su. Hukumar ta ce likitoci sun shaida cewa lallai irin wadannan tsofaffi sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar.

Haka zalika, idan ba a manta ba, gwamnan Jigawa Mohammed Badaru ya shaida cewa jihar ta sallami duka wadanda suka kamu da cutar.

Gwamna Badaru ya ce mutum daya ne tal ya rage a jihar bai warke ba tukunna.

Share.

game da Author