KORONA: Mutum 51 sun rasu, an sallami 718 a jihar Kano

0

Ma’aikatar kiwon lafiyar jihar Kano ta bayyana cewa mutum daya ya mutu a dalilin kamuwa da cutar Korona sannan an sallami mutum shida da suka warke daga cutar a jihar.

Hakan ya kawo adadin yawan mutanen da suka mutu zuwa 51 sannan wadanda aka sallama kuma zuwa 718.

A yanzu haka akwai mutum 1,190 dake killace a asibiti ana ci gaba da duba su.

A ranar Litini ma’aikatar lafiya ta ce ta yi wa mutum 1,466 gwajin cutar a wuraren yin gwaji biyar dake fadin jihar sannan kuma gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya ce jihar na samun nasara a yakin dakile yaduwar cutar.

Ya ce a makon da ya gabata jihar ta yi wa mutum 2,603 gwajin cutar inda daga ciki mutum 140 sun kamu.

Ganduje ya yi kira ga mutane da su ci gaba da bin sharuddan gujewa wa kamuwa da cutar domin a iya dakile yaduwar cutar Kwata-kwata a jihar.

Alkaluma sakamakon gwajin cutar da Hukumar NCDC ta fitar ranar Litini ya nuna cewa mutum 675 sun kamu da cutar a kasar nan a wannan Rana.

Wannan karo babu wanda ya kamu da cutar a jihar Kano.

Yanzu mutum 20,919 suka kamu da cutar kuma an sallami mutum 7109 a Najeriya.

Hukumar ta ce ana samun Karin yawan mutanen da suka kamu da cutar ne saboda gwaji da ake yi wa mutane akai-akai a fadin Kasar nan.

Share.

game da Author