A daidai wannan lokaci da Covid-19 ke dada yaduwa a kasar nan kamar wutan daji, Kungiyar likitoci ‘ARD’ ta fara yajin aikin gama gari.
kungiyar ta sanar da fara yajin aikin a daidai yawan lambar mutanen da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ya zarce mutum 16,085sannan sama da mutum 400 sun rasu.
Shugaban Kungiyar Roland Aigbovo ya tabbatar da fara yajin aikin wa PREMIUM TIMES.
Idan ba a manta ba, tun a farkon barkewar annobar Korona Likitocin suka yi barazanar fara yajin aiki dalilin kin biyan su albashi na wata biyu da zaftare mutu musu kudade da gwamnati ke ta yi.
A Wannan lokaci rashin biyan likitocin albashinsu na tsawon watanni biyu da zaftare musu babban kaso daga cikin albashinsu na daga ciki dalilan da ya sa Kungiyar Za ta fara yajin aiki.
Kungiyar ta ce gwamnati ta zaftare musu kaso mai yawa daga albashin su duk da sun yi rajista a tsarin biyan albashi na ma’aikatun gwamnatin tarayya, IPPIS.