Kwamitin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa domin nemo hanyar ceto tattalin arzikin Najeriya bayan barkewar cutar Coronavirus, ya bayyana cewa kasar nan ta kusa ruftawa halin matsin da ba ta taba shiga ba a baya.
Yayin kwamitin ke damka wa Buhari rahoton sa, ya ce Najeriya na fuskantar gagarimar matsalar tattalin arziki wadda ba ta taba shiga irin ta ba a tarihin kasar.
A ranar 30 Ga Maris ne Buhari ya kafa kwamitin mai mambobi 9, domin gano mafitar yadda yadda za a hana tattalin arzikin kasar nan ruftawa rami gaba dubu.
An kuma bai wa kwamitin nauyin fito da wasu hanyoyin da gwamnatin tarayya za ta rage kashe makudan kudade barkatai, sai fa a hanya ko bangaren da ya zama dole.
An umarci kwamitin ya shata layin da zai hana kasar nan afkawa cikin hauragiyar korar ma’aikata, ta hanyar nemo yadda za a tallafa wa masana’antu da kuma jihohin kasar nan 36 da Babban Birnin Tarayya, FCT.
Mugun Ji Da Mugun Gani:
PREMIUM TIMES ta ga kwafen kundin rahoton kwamitin mai shafuka 76.
Rahoton ba shi da dadin gani ko karantawa, domin ya bayyana irin halin kalubalen tattalin arzikin da kasar nan za ta fuskanta gadan-gadan.
Matsalolin sun nuna wani wawakeken rami ne Najeriya ta dumfara a sukwane, yayin da linzamin dokin ya kubce, yadda babu makawa sai an rufta – sai fa idan an yi wani namijin kokari.
Dalla-dallar Abin Da Kwamiti Ya Rubuta A Takaice:
1. Najeriya na fuskantar wani mummunan halin gurguncewar tattalin arziki, wanda ba ta taba shiga irin sa a baya ba.
2. Saboda annobar cutar Coronavirus ta rike wa kusan kowace kasa wuya, kusan duk wata kasar da za a iya neman hadin-guiwar ceto Najeriya da ita, to ita din ma ta-kan-ta ta ke yi.
3. Matsalar bangaren lafiya ta haifar da rugujewar tattalin arzikin fannoni da dama. Jari ya kak-karye, rashin aikin yi na ta karuwa, saboda yadda ake yawan sallamar ma’aikata bagatatan.
5. Sakacin da aka yi Najeriya ba ta dogara da komai ta fannin kudaden shiga ba, sai man fetur ya kara haifar wa kasar gagarimar matsala.
6. Faduwar farashin danyen man fetur ta yadda tun ana sayar da ganga daya dala 12, har farashin gangar ya dawo daidai da farashin sauran ruwan aski, ya sacce tayoyin tattalin arzikin Najeriya a inda babu mai faci a kusa.
7. Yayin da ba a samun kudin shiga a kasuwar danyen man fetur ta cushe. Ta kai lokacin da ko sisi ba a samu da sunan kudin shiga a gas (NNLG).
8. Wato a yanzu hanyar samun kudaden shiga daga waje ta toshe, sannan kuma asusun ajiyar Najeriya na waje ba wata habbaka ya ke yi ba. Maimakon haka, raguwa ma yake yi saboda biyan kudade da Najeriya ke yi a waje da kuma shigo da kayayyaki daga waje da ake yi.
9. Kudaden harajin cikin da kasar nan ke tutiya, yanzu babu, kuma ba a samu. Domin annobar Coronavirus ta tsaida komai, an rufe harkokin kasuwanci da hada-hada a Lagos, Ogun da Kano da ma sauran jihohi. Wannan ya haddasa rashin samun kudin shiga da kuma rashin aiki.
10. Farashin dala ya yi sama, darajar naira ta kara faduwa warwas a kasuwar hada-hadar musayar kudi. Ga kuma tashin farashin kayan da ake shigowa da su daga waje, a daidai lokacin da karfin nauyin aljihun ‘yan Najeriya ya ragu sosai, saboda rashin samun kudi da aka shiga.
11. Duk wata babbar harkar da ya dogara da shigo da kayan aiki daga kasashen waje, ta shiga jula-jula saboda farashin komai ya tashi.
12. Ko kafin ma barkewar cutar Coronavirus, tattalin arzikin kasar nan tuma tsalle wuri daya kawai ya ke yi. Saboda kudaden ribar danyen mai da ake samu, kusan rabin kudin duk a wajen biyan basussuka su ke tafiya. Saboda haka da annobar Coronavirus ta barke a kasar nan, iska ne ya zo ya iske kaba na rawa.
Ci Gaban Bayanan Kalubale:
Kwamitin Osinbajo ya ci gaba da bayanin cewa akwai manyan kalubale da suka baibaye kasar nan.
Ya buga misali da awon mizanin da ya ce sama da mutum milyan 40 a kasar nan tantiran talakawa ne da ko sun fita sun yi gumi sun yarfe, sun nemi na kan su, to ba za su iya samu naira 137,000 a shekara daya cur ba.
Sannan kwamitin ya rika yin bugun kasa ya na hisabi ya na shafewa. Sannan kuma ya sake bugawa ya nemi sa’a, ya shafe.
A wannan bugun kasar, Kwamitin Osinbajo ya rika kirdado da kintacen abin da Najeriya za a iya samu a shekara idan ta sayar da danyen man fetur a farashi daban-daban da kwamitin ya rika yin bugun-kasa da su.
Sai dai kuma duk lissafin da ya yi, a karshe amsar da ya ke gani ita ce babu wata mafita, sai ma kara afkawa cikin surkukin jejin matsin tattalin arzikin kasa.