Kodinatan kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa yanzu fa tura ta kai bango kan matsalar tsaro a Arewa domin mutanen yankin na shan azabar mahara da ‘yan bindiga.
Abdullahi ya ce, in banda cika baki da gwamnatin Buhari ke yi, sannan a kullum ana kashe mutane kamar kaji a yankin babu wani nasara da take samu.
Ya ce mutane sun gaji da cika bakin gwamnatin Buhari.
” Yadda mahara da ‘Yan bindiga suke cin karen su ba babbaka a yankin Arewa yanzu ya sa mutane ba su da karfin yin komai sai yadda suka yi da su. Su afka wa kauye su kashe da kashewa, su sace na sacewa sannan su yi tafiyar su lafiya lau, gobe sai a fito a ce ana gama da su, a ina a ka gama da su?
” Karara dai ya nuna gwamnatin Muhammad Buhari da gwamnoni musamman na yankin Arewa fa abin ya fi karfin su. Ba za su iya tabbatar da tsaro a yankin Arewa ba, wanda shine hakkin da ya rataya a kan su.
” Abin yanzu yayi tsanani matuka domin su kan su maharan sun gane akwai wawukeken gibi a harkar tsaro a kasar nan da ya sa sukan yi abinda suka ga dama babu waiwayen baya. A matsayin mu na dattawan Arewa muna tare da miliyoyin yan Najeriya dake kwana addu’a Allah ya kawo mana karshen wannan matsala na tsaro a Kasar nan sannan da rokon mahukunta da hakkin haka ya rataya a kansu su samar wa mutane tsaro kamar yadda suka yi alkawari.
” Lokaci yayi da dole mu fito muce wahalar ya isa haka. An san mutanen mu da bin doka da oda. Amma ya kamata gwamnati ta sani tura ya kai bango yanzu. Akwai yiwuwar a fita a yi gangami na zanga-zanga wanda doka ta basu damar haka domin jawo hankalin shugaba Muhammadu Buhari da mahukunta su saurari kukan mutane.
” Matsalar da muka shiga a Arewa ya tabbatar mana da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaza, ba za ta iya ba, wannan shine gaskiyar magana. Ba za mu yarda da haka ba. Gwamnati ta inganta tsaro a yankin Arewa shine damuwar mu. Mun gaji da cika baki, Kullum ace an gama da su ko kuma an yi nasara bayan karara, kowa na gani an gaza, abu dai ya fi karfin mahukuntar wannan gwamnati.