Kwamitin Zartaswa na Kasa na Jam’iyyar APC, ya nada Gwamna Mai Mala Buni na Yobe a matsayin Shugaban Rikon Kwarya na Jam’iyyar APC na Kasa.
Nada shi ya biyo bayan sauke Kwamitin Gudanarwa na Kasa na APC da aka yi, wanda ke karkashin shugabancin Adams Oshiomhole, wanda kotu ta jaddada dakatar da shi daga jam’iyyar.
An dora wa Buni ci gaba da rikon ragamar APC duk da nauyin rikon jihar Yobe da ke hannun sa.
Buni shi ne Sakataren APC na Kasa har zuwa 2019, lokacin da ya zama gwamnan jihar Yobe.
Mataimakin Sakataren APC na Kasa, Victor Giadom ne ya kira taron wanda shi ne ya yi ikirarin zama Shugaban Riko a lokacin da Babbar Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta jaddada dakatarwar da aka yi wa Adams Oshiomhole daga jam’iyyar APC a mazabar sa cikin Karamar hukumar sa a jihar Edo.
NEC dai shi ne kwamiti na biyu mafi girma a APC, baya ga taron gangamin jam’iyya na kasa.
Sai dai kuma akasarin mambobin Kwamitin Gudanarwa ba su goyi bayan taron ba, wanda Giadom ya kira, sun ce shi ma ba halastaccen mamba din NWC ba ne.
Idan ba a manta ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayan sa ga shugabancin tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Kudu-Maso-Kudu, Victor Giadom.
Kakakin fadar shugaban Kasa, Garba Shehu ya sanar da haka a takarda da ya fitar ranar Laraba.
” Buhari zai halarci taron jam’iyyar wanda Giadom ya kira saboda shine yanzu shugaban jam’iyyar, kamar yadda kotu ta yanke hukunci.
” Kwararru sun ba shugaba Buhari shawara mai zurfi game da badakalar shugabancin jam’iyyar a yanzu. Kuma yabi wannan shawara da khudubobin su dalla-dalla. A karshe dai hankalin sa ya fi kwanciya kan shugabancin Giadom a matsayin shugaban jam’iyyar na wucin gadi bisa hukuncin kotu.
Kamar yadda Shehu ya fadi, ana sa ran shugabannin jam’iyyar, gwamnoni da ‘yan majalisu za su halarci wannan taro.
Kotu ta yanke hukuncin Giadom ne shugaban jam’iyyar na tsawon makonni biyu da za su zo. Amma kuma jam’iyyar ta garzaya kotu ita ma inda ta sa kotu ta ba da izinin jingine hukuncin wancan kotun.
Giadom dai ya lashi takobin lallai shine shugaban jam’iyyar APC a yanzu.
Idan ba a manta ba kotun daukaka kara ta dakatar da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole daga jam’iyyar a dalilin hukuncin dakatar da shi da kotu ta yi a baya.
Tun daga mazabar sa da karabar hukumar sa ta Etsako West wakilan jam’iyyar suka dakatar da shi wanda hakan ya ba kotun daukaka kara daman jaddada hukuncin dakatar da shi da kotu ta yi.
Duka da cewa jam’iyyar ta rattaba hannu cewa sanata Abiola Ajimobi ne shugaban ta na rikon kwarya, Giadom ya yi watsi da jam’iyyar ya nada kansa shugaban jam’iyyar na wucin gadi.