Tsohon ministan sufurin jiragen Saman Najeriya, Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa yanzu dai ta nuna kakara cewa ruwa ya kare wa dan kada, wato Tinubu dai ta kare masa.
Fani-Kayode ya ce yanzu dai APC ta jefar da Tinubu cikin kwandon shara sannan an yi masa murabus a siyasa da karfin tsiya.
Bola Tinubu jigo ne a siyasar Najeriya kuma jiga a jam’iyyar APC. Yana daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC bayan hadewa da tayi da CPC kafin zaben 2015.
Tinubu da ministan sufuri, Rotimi Amaechi ba su ga mai maciji a tsakanin su tun da dadewa, da hakan yai sanadiyyar wancakalar da babban aminin Tinubu daga shugabancin Jam’iyyar APC wato Adams Oshiomhole.
Fani-Kayode ya ce, gashi dai an tsige shugaban jam’iyyar APC, Oshiomhole wanda aminin Tinubu ne, Jam’iyyar APC ta nada Mai-Mala Buni shugaban riko, kaga ko ai yanzu ruwa ya kare wa Tinubu, sun yi masa murabus a siyasa.
Idan baa manta ba, tun bayan kotu ta tsige Oshiomhole da kotu tayi, jam’iyyar APC ta rufta cikin kamayamayar rugujewar, wancan ya fito ya ce shine wane, wancan ya ce a’a shine wane.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda shine shugaban jam’iyyar karkaf, karkata zuwa ga bangaren Victor Giadom da ya nada kansa shugaban jam’iyyar.
Bayan gudanar da ganawar su na ranar Alhamis, jam’iyyar ta nada gwamnan Yobe Mai Mala Buni shugaban riko har sai an yi taron gangami na kasa.