Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Najeriya ta ce za a kwaso ‘yan kasar nan su 265 daga Dubai, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Kakakin Yada Labarai na Ma’aikatar Harkokin Waje, Ferdinand Nwonye ne ya fitar da sanarwar wannan labari a ranar Talata, 5 Ga Mayu.
Ana sa rann isowar su a ranar Laraba, karfe 3 na rana a filin Murtala Mohammed da ke Lagos.
Tuni dai an rigaya an tanadar musu otel a Lagos da Abuja, kamar yadda sanarwar ta sanar.
“Dukkan otal din da za su sauka sai da aka tura jami’an tsaro tare da jami’an kula da lafiya da na Hukumar NCDC, suka bincike su tukunna. Dukkan su dai Emirate Airline ne zai kwaso su.
Sanarwar ta kara da cewa an kuma daidaita za a kwaso wasu ‘yan Najeriya su 300 daga London, jigilar da jirgin British Airways zai yi a ranar Juma’a mai zuwa.
Haka nan idan ba a manta ba, ranar 11 Ga Mayu ne za a fara kwaso ‘yan Najeriya daga Amurka.
Mutane masu dimbin yawa ne suka makale a kasashe daban-daban tun bayan da Najeriya ta kulle filayen jiragen ta.
‘Yan Najeriya da dama sun makale a kasashen waje a dalilin annobar coronavirus.
Kasashen duniya sun dakatar da tashi da saukan jiragen saman kasashen su da na wasu kasashen.
Mafi yawan su ba mazauna can bane, an rufe gari ne da su a daidai sun kammala abinda ya kai su, dawowa ya gagara.