Gwamnatin Jihar Jigawa ta nuna matukar damuwa da fargabar yadda ake yawan samu masu dauke da cutar Coronavirus a jihar.
A ranar Talata ta ce fantsamar cutar a cikin al’umma na kawo barazana sosai ga rayuwar dimbin jama’a.
Sannan kuma gwamnatin ta nuna fargaba dangane da yadda ake yawan mace-mace a jihar, mutuwar da har yau an kasa gane dalili ko musabbabi.
“Sabbin adadin alkaluma 32 da aka samu a jihar Jigawa, ba daga almajirai aka same su ba. Duk an same su ne daga cikin jama’a. Saboda haka matsawar jama’a ba MU ciki gaba da addu’o’i da zaman gida da kuma kiyayewa da sauran ka’idojin kauce wa kamuwa da cutar ba, to za ta ci gaba da yaduwa a cikin jama’a.”
Haka wani hadimin Gwamna Badaru Abubakar, mai suna Zakari Kafin Hausa ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Yayin da Coronavirus ke ciki gaba da fantsama, kuma mutane ba su kiyayewa da dokoki da ka’idoji, a ranar Talata an samu adadin wadanda suka kamu a rana daya zuwa 254, inda 32 daga cikin su a jihar Jigawa su ke.
“Yawancin wadanda ake samu da cutar nan, idan aka debi sinadarin jikin su aka kai awo, akan gargade su cewa su zauna wuri daya su killace kan su.
“Sannan da yawan mutane ba su ma yarda akwai ta ba. To ka ga irin haka ke haddasa karin yaduwar cutar da fantsamar ta cikin jama’a.”
Yawan Mace-mace:
Gwamna Badaru ya tabbatar da cewa an samu rahoton mace-mace a Kazaure, wadanda ba a san ko a ce an gano dalili ba.
Amma ya ce han kafa wani kwamiti tare da jami’an Hukumar Lafiya ta Duniya domin binciko ko mace-macen na da akala da Coronavirus, ko wani abin dban.
Ranar Talata, jaridar Daily Trust ta buga labarin cewa, “Mutum 100 sun mutu a Jihar Jigawa Cikin Kwanaki 10.”
Discussion about this post