WATA SABUWA: Masu fama da Coronavirus sun yi Zanga-Zanga a Gombe, sun datse manyan tituna

0

Wasu marasa lafiya da ke fama da cutar Coronavirus sun datse manyan titunan garin Kwadon dake karamar hukumar Yamaltu Deba, inda suka koka da watsi da gwamnati ta yi dasu tun bayan killace su.

Marasa lafiyan sun ce kwata-kwata ba a basu kula. Tun da aka killace a wani gida a garin Kwadon aka yi watsi da su.

Masu zanga-zangan sun ce maimakon a ci gaba da killace su ba a yi musu komai, gara a kyalesu su ci gaba da hidimomin su kawai. kowa ya koma gida.

Mazauna wannan garin na Kwadon sun tsorata matuka, inda suka koka da yin kira ga gwamnati da su gaggauta kawo wa wadannan marasa lafiya dauki domin wannan abu da suka yi akwai hadari a ciki matuka.

” Mutane da dama sun tsorata a wannan gari kowa yana nesa-nesa domin gudun kada a kamu da cutar.

Saidai kuma kwamishinan yada labarai na jihar, Alhassan Ibrahim Kwami ya bayyana cewa ba watsi da su gwamnati ta yi ba.

” A halin da suke ciki, ba su kai arika basu magani ba tukunna domin cutar bata bayyana a jikin su ba sai dai ya nuna sun kamu a gwajin samfarin su da a kayi.

” Wannan shine ya sa gwamnati ta killace su tana kula da su. Amma bai kai a rika basu magani ba tukunna. Amma gwamnati zata gaggauta duba matsalar da yake tattare da marasa lafiyan domin magance shi.

Share.

game da Author