Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana cewa sama da ‘yan Najeriya miliyan 82.9 na fama da tsananin talauci.
NBS ta bayyana haka a rahitan da ta fitar ranar Litini game da matsayin talaucin ‘yan Najeriya.
Hukumar ta ce akalla kashi 40.1% na yan Najeriya matalauta ne tuburan.
Jihohin Sokoto, Taraba, Jigawa, Ebonyi, Zamfara, Yobe da Adamawa suka fi fama da talauci a Najeriya.
Kashi 87.73% na mutanen Sokoto talakawa ne, sai jihar Taraba dake da kashi 87.73% na mutane fakirai, sai jihar Jigawa dake da 87.02%, sai kuma jihar Ebonyi dake da kashi 79.76% na talakawa.
Alakaluma daga rahotan ya nuna cewa jihohin Legas, Delta, Osun, Ogun, Oyo, Edo da Anambra sun fi karancin Talakawa a Najeriya.
Bayan haka, an fi samun matalauta a karkara fiye da birane a bisa wannan rahoto.
Idan ba a manta ba Hukumar NBS, ta ce farashin kayayyaki, wanda da su ne ake gane kuncin rayuwa ko yalwar arziki, sun nuna cewa kuncin rayuwa a Najeriya ya yi karuwar da bai taba yi ba tsawon watanni 23.
Ya zuwa watan Maris, an jera watanni bakwai a jere duk wata sai farashin kayayyaki sun tashi. Wannan kuwa na da nasaba da rufe kan iyakokin Najeriya da aka yi, sai kuma kulle garuruwa da aka yi a lokacin Coronavirus.
Rahoton Tashin Gwauron Zabon Farashin Kayan Masarufi ya tabbatar cewa an samu tashin farashi zuwa kashi 12.26.
Farashin kayan masarufi da abinci sun rika tashi tun.daga watan Satumba, 2019, bayan an rufe kan iyakokin kasar nan cikin watan Agusta, 2019.
Kulle kan iyakokin ya haifar da karin farashin shinkafa, man girki, abincin gwangwani nau’uka daban-daban da sauran kayan masarufi.
“Garkame Abuja, Lagos da Abuja ya haifar da tsayawar al’amurran aiki, sufurin kayan masarufi da sauran harkokin jigila da aikace-aikace.” Inji NBS.