Bayan rasuwar Sarkin Rano Tafida Illa a makon daya gabata, gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya nada Hakimin Kibiya, Kabiru Inuwa sabon Sarkin Rano.
Masu nada sarakuna a masarautar Rano sun aika da sunayen Muhammadu Umar (Hakimin Bunkure) da Munir Abubakar (Chiroman Rano).
Ganduje ya hori sabon sarkin ya yi mulki da adalci.