Ibrahim Gambari ya fara aiki gadan-gadan

0

Sabon Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari ya fara aiki gadan-gadan a fadar shugaban kasa.

Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya sanar da nadin Gambari tunda sanyin safiyar Laraba a shafin sa ta tiwita.

Hakan ya tabbatar da labarin PREMIUM TIMES da ta buga, cewa tun jiya Talata iyalai da ‘yan uwan sabon Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa suka tabbatar da nadin Gambari.

Sarkin Ilori, ya tabbatar da haka Inda tun a jiya ya aika wa shugaban kasa Buhari da wasikar godiya bisa nadin Gambari da yayi shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa.

Tuni dai fitacce, kuma sanannen ma’aikaci, Farfesa Gambari ya bayyana a fadar shugaban Kasa domin fara aiki.

Dashi a ka bude taron majalisar zartaswa da aka yi ranar Laraba a fadar shugaban Kasa Inda tun da sassafe ya dira Aso Rock domin fara aiki gadan-gadan.

Share.

game da Author